Hari a kan sojojin ketare a arewacin Mali
November 30, 2020Talla
Majiyar sojin Malin da ta ruwaito harin harin na wannan Litinin, ta kara da cewar ba kasafai ake ganin irinsa ba a lokaci guda kuma a wurare daban daban.
Mai magana da yawun rundunar sojin faransa da ke sa jami'ai sama da dubu biyar a Sahel Thomas Romiguier ya bayyana cewar, harin ya ritsa da ginin MDD da ke Kidal wadda ke kusa da sansanin sojin Faransan.
Kasar ta yankin yammacin Afirka dai na fama da matsalolin tsaro daga hare haren mayakan da ke kiran kansu na "Jihadi", rikicin da ya samo tushe daga arewaci kuma sannu a hankali ya bazu zuwa kasashe makwabta na Burkina Faso da Nijar.