MDD ta kakabawa Boko Haram takunkumi | Labarai | DW | 23.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta kakabawa Boko Haram takunkumi

Bisa ga bukatar Najeriya ne dai wakilan Komitin Sulhu goma sha biyar suka amince da matakin sanyawa wannan kungiya takunkumi.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya kungiyar Boko Haram cikin jerin kungiyoyin ta'adda kamar al-Qaeda. Wannan mataki ya biyo bayan bukatar da gwamnatin Najeriya ta gabatar ne kan sanya kungiyar a jerin kungiyoyin ta'addanci. Dukkan wakilai 15 na komitin sulhun dai sun gamsu da wannan mataki. Kazalika an sanyawa kungiyar takunkumin sayen makamai da hanasu taba kaddarorinsu da tafiye tafiye. Sama da mutanme 100 ne dai suka rasa rayukansu a wannan makon kadai, a hari daban daban a cikin garin Jos na jihar Plateau da kuma wani gari kusa da Chibok da ke jihar Borno. Sama da wata kenan 'yan kungiyar ke ci gaba da tsare 'yan mata sama da 200 da suka sace a jihar ta Borno.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman