MDD ta gargadi Iran kan gwajin makamai | Labarai | DW | 10.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta gargadi Iran kan gwajin makamai

Babban sakataren majalisar Ban Ki-moon ya yi kira ga Iran da ta yi taka tsantsan dangane da matakanta na gwajin makamai masu linzami.

Kiran Majalisar Dunkin Duniyar na zuwa ne bayan gwajin makamai masu linzami na kwanaki biyu da Tehran ta yi cikin mako guda.

Ban ya ce bisa la'akari da halin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki, kana lokaci kalilan bayan cimma nasarar dagewa Iran din takunkumi, akwai bukatar mutuntawa tare da nuna halin sanin ya kamata a bangaren wannan kasa ta Janhuriyar Islama.

A cewar kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarri, bai kamata kasar ta Iran ta ruruta wutar rikicin da yankin na gabas tsakiya ke ciki a halin yanzu ba.