1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta cika shekaru 75 da kafuwa

Abdul-raheem Hassan
September 21, 2020

Shugabannin duniya za su gudanar da taron cika shekaru 75 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya ta yanar gizo, ranar ta zo lokacin da annobar Corona ta kassara ayyukan jin kai na kungiyar mai mambobi 193 a duniya.

https://p.dw.com/p/3ilva
UN-Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: Imago Images/Xinhua/

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce wannan shi ne lokaci mafi dacewa da duniya za ta hada karfi da karfe a samar da mafita kan tarin matsalolin da annobar ta jefa duniya ciki.

Sauran kasashe 15 a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun jajirce don mara wa yunkurin Guterres baya na tsagaita bude wuta a kasashen da ke fama da yaki domin maida hankali kan kawar da cutar Corona.