MDD ta ce soji su kaucewa shiga siyasa Iraki
August 11, 2014Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Jamian tsaro a Iraki da kada su tsoma bakinsu a harkokin siyasar kasar bayan da shugaban kasar ya bayyana sunan wanda zai maye gurbin al-Maliki a matsayin sabon firaminista.
Jakadan MDD a Iraki Nickolay Mladenov shi ya bayyana haka: "Duk wani yunkuri da zai sanya a ga hannun soji a harkokin siyasar kasar abin kyamane".
Bayan da shugaba Masum ya amince da zabin kawancen jamiyyar bangaren 'yan shia da suka amince da Haidar al-Abadi,magoya bayan Maliki sun tattaru a tsakiyar birnin Baghadaza dan nuna adawarsu.
Tun ma dai a yammacin ranar Lahadi ne aka samar da jamian tsaro na farin kaya da 'yan sanda da soji a wasu fitattun wurare a birnin na Baghadaza kafin daga bisani Nuru al-Maliki ya bayyana a kafar talabijin cewa zai gurfanar da shugaban kasar a gaban kuliya idan yaki bayyana shi a matsayin firaminista.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba