1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD: Rikici ya raba mutane miliyan 14 da gidajensu a Afirka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 20, 2024

MDD ta ce kididdigar ba ta kunshi Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo ba, inda mutane miliyan 7 suka bar gidajensu

https://p.dw.com/p/4kspU
Hoto: UNCHCR

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da rikici ya tilastawa tsere wa daga muhallansu a tsakiya da kuma yammacin Afirka ya tasanma kai wa miliyan 14, wanda ya ninka yawansa tun daga 2019 zuwa yanzu.

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, mai kula da shiyyar tsakiya da yammacin Afirka Abdoraouf Gnon-Konde, ya ce a baya dai wato a shekarar 2019, adadin ya tsaya ne a kan miliyan 6 da rabi, kafin ya kai miliyan 13 da dubu dari bakwai.

Karin bayani:'Yan gudun hijira 38 sun rasu a kogin Djibouti

Mr Konde ya ce kididdigar ba ta kunshi Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo ba, inda mutane miliyan 7 suka bar gidajensu.

Chadi da ke zama daya daga cikin kasashe matalauta a duniya, na cikin halin tsaka mai wuya, bayan da ta karbi 'yan gudun hijira dubu dari shida da hamsin daga Sudan, mai fama da yakin basasa tun cikin watan Afirilun bara.

Karin bayani:'Yan Sudan suna fatan kawo karshen yaki

Haka dai batun yake a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, masu fama da hare-haren ta'addanci, inda mutane miliyan biyar na kasashen suka tsere daga gidajensu.