1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira 38 sun rasu a kogin Djibouti

Abdullahi Tanko Bala
April 9, 2024

Dubban 'yan gudun hijira ne daga Afirka suke kokarin zuwa kasashen yankin tekun fasha a kowace shekara ta tekun Bahar Maliya. Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana hanyar a matsayin mai matukar hadari.

https://p.dw.com/p/4easa
Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM
Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOMHoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

A kalla 'yan gudun hijira 38 ne suka rasu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a gabar kogin Djibouti a cewar kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM.

Kungiyar ta ce wasu mutanen shidda sun bace ba a gan su ba, sai dai ana kyautata zaton su ma sun mutu. Sai dai kuma an sami nasarar ceto mutane 22.

A kowace shekara dubban 'yan gudun hijira ne suke barin yankin kahon Afirka, yawancinsu daga Habasha da Somalia inda suke kokarin zuwa kasashen yankin tekun fasha  a cewar Yvonne Ndege mai magana da yawun kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya.