Yakin Idlib ya tagayyara dubban jama'a
February 14, 2020Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yan Syria fiye da dubu 140 aka tagaiyara cikin kwanaki a yakin da ke cigaba da gudana a Idlib wanda ya kaswo adadin mutanen da suka tagaiyara zuwa dubu dari takwas.
Majalisar Dinkin Duniyar ta ce kashi 60 cikin dari na mutanen dubu 800 da aka tagaiyara a watan Disambar bara yara ne kanana.
A nasa bangaren Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas yace wajibi ne a kawo karshen hare haren da ke gudana a Idlib. Ya bukaci samo hanya ta masala domin warware rikicin.