1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci tsara rigakafin corona

Abdullahi Tanko Bala
February 17, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran tsara wani jadawali na bai daya a yunkurin da ake yi na samar da allurar rigakafin Corona ga daukacin kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/3pVNF
USA I UN-Generalversammlung I Antonio Guterres
Hoto: UNTV/AP/picture-alliance

Majalisar ta yi gargadin cewa rashin daidaito wajen samun maganin na iya jefa duniya cikin hadari.

Ministocin harkokin waje da suka halarci taron da aka gudanar a karon farko ta yanar Gizo karkashin jagorancin Birtaniya sun baiyana cewa wannan hakki ne da ya rataya a wuyan kasashen duniya baki daya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya nuna damuwa cewa kasashe 10 ne kacal daga cikin kasashe 130 suka aiwatar da 75 cikin dari na allurar rigakafin ya zuwa yanzu.