MDD: Kasashe bakwai sun rasa damar kada kuri′a | Labarai | DW | 18.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Kasashe bakwai sun rasa damar kada kuri'a

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta dakatar da kasashe bakwai saboda rashin biyan kudin karo-karo na tafiyar da ayyukan majalisar.

Kasashen bakwai da suka hada da Iran sun rasa damar kada kuri'a a babbban zauren Majalisar Dinkin Duniya saboda rashin biyan da aka saba, kamar yadda Antonio Guterres babban sakataren majalisar ya bayyana a wannan Litinin.

Wani kudiri na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci dakatar da kuri'ar da kasa za ta iya kadawa muddun ta gaza biyan kudin da aka tsara ake bai wa majalisar tsakanin kasashen duniya inda rashin biyan ya wuce shekara biyu.

Sauran kasashe shida su ne: Jamhuriyar Nijar, Libiya, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kwango Brazzaville, Sudan ta Kudu da Zimbabuwe kamar yadda babban sakataren ya rubuta ga shugaba babban zauren majalisar Volkan Bozkir dan kasar Turkiyya.