1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: A tsagaita wuta a Ghouta

February 23, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta sake kira da babbar murya ga bukatar tsagaita tsananin luguden wuta da ke wakana a gabashin Ghouta na wajen birnin Damascus na kasar Syria.

https://p.dw.com/p/2tE9W
Schweiz UN Friedensgespräche für Syrien
Manzon Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Staffan de MisturaHoto: picture-alliance/Photoshot/Xu Jinquan

Manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura ya ce lallai ne gwamnatin shugaba Bashar al Assad ta tsagaita wannan tsananin, don bada damar kai akalla kayan agaji da kuma kwashe wadanda hare-haren suka tagayyara. Cikin wata takardar da ya aike wa taron MDD a birnin Geneva, Mr de Mistura, ya ce tilas ne kasashen da suka sanya hannu a taron neman zaman lafiya na birnin Astanan kasar Kazakhstan, su gaggauta zama don sake samar da tuddan mun tsira a Syriar.

Manzon na Majalisar ta Dinkin Duniya, na magana ne 'yan sa'o'i gabanin kuri'ar da kwamitin sulhu zai kada a kan samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30 a Syria.