Mazauna Bama na kauracewa muhallansu | Labarai | DW | 02.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mazauna Bama na kauracewa muhallansu

Fada na ci gaba da tsamari tsakanin dakarun sojan Najeriya da mayakan Boko Haram, abinda ya sanya dubban al'umma ke ficewa daga yankin Bama na jihar Borno.

Dubban jama'a ke kauracewa muhallansu a garuruwan da Kungiyar Boko Haram ta bayyana cewa ita ke da iko da su, wannan kuwa na zuwa ne adaidai lokacin da fada ke kara kazanta tsakanin dakarun sojan Najeriya da mayakan sakai na kungiyar.

Mayakan na Boko Haram sun kaddamar da hari a garin Bama wanda ke da tazarar kilomita 70 daga Birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno arewa maso gabashin Najeriya. A ranar Litinin dakarun na Boko Haram sun ja da baya daga bisani cikin dare suka kawo farmaki tare da yawan mayaka kamar yadda wasu shedun gani da ido suka shedar.

Babu dai wani martani daga bangaren mai magana da yawun sojan na Najeriya, sai dai rahotanni na nuni da cewa dukkanin bangarorin biyu sun rasa dakaru a gwabzawar da suka yi wacce ta yi sanadin ficewar kimanin mutane 5,000 daga yankin da fadan ya yi tsamari.

Watanni biyu bayan da mayakan Islama a Iraki da Syria suka bayyana kafa daular Musulinci, Boko Haram ta yi ikirari na kafa daula a yankunan da ta ce tana da iko da su a arewa maso gabashin Najeriya.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Usman Shehu Usman