Mayaka sun kashe sojojin Burkina Faso | Labarai | DW | 22.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayaka sun kashe sojojin Burkina Faso

Babu kungiyar da dau alhakin harin da ya kashe sojojin a lokacin da suke aikin sintiri, sai dai jami'an tsaro sun sha alwashin daukar fansa.

Rahotanni daga Ougadugu babban binrin kasar Burkina Faso na cewa akalla sojoji hudu sun mutu wasu 12 sun jikkata a wani harin kwantan bauna da mahara dauke da manyan makamai suka kaddamar.

Kasar Burkina Faso na cikin kasashen yankin Sahel da ke fuskantar barazanar mayakan jihadi tun bayan da suka kaddamar da kai hare-hare a kasar Mali a shekarar 2015.