Mayaka sun kai hari Gombi-Adamawa | Labarai | DW | 14.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayaka sun kai hari Gombi-Adamawa

Wasu yankunan Arewacin Adamawa sun fuskanci sabbin hare-hare tun daga daren jiya Alhamis, a daidai lokacin da wani jirgi ya sake faduwa a Girei kusa da Yola

Mayakan da ake zargin na Boko Haram ne sun kai wani hari a karamar hukumar Gombi dake Jihar Adamawan Nigeria. Rahotanni daga yankin dake arewaci dai, na nuni da cewar mayakan sun yi ta harbin bindigogi, wanda ya haddasa daruruwan mutane ficewa tun a daren Alhamis.

A yanzu haka mazauna garin na cikin garin da basu tsere ba na ci-gaba da zama cikin fargaba. Kazalika mazauna garuruwan da ke makwabtaka sun fara kauracewa nasu matsugunnen sakamakon rashin sanin me zai biyo baya.

Wannan hari dai na zuwane jim kadan bayan da gomnatin jihar ta baiyana nasara kwato garuruwan Mubi da Maiha dake hannun kungiyar.

A hannu guda kuma wani jirgi da ake zaton yana dauke da makamai ya fado a garin Girei dake kusa da Yola fadar Jihar Adamawa a daren Alhamis.