Mawaƙa nawa ne suka rera waƙar ″We are the World″? | Amsoshin takardunku | DW | 09.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Mawaƙa nawa ne suka rera waƙar "We are the World"?

Waƙar "We are the World" dai kamar yadda aka sani, waƙa ce da wasu mawaƙan zamani suka rera a shekarar 1985

default

Marigayi Michael Jackson

Tambaya ta farko ta fito ne daga hannun Sani Maibeka Rijiyar Lemu Kano, wanda ke son a ba shi tarihin waƙar nan ta “We are the World”, da kuma dalilin rera wakar da kuma shekarar da aka rera ta da kuma mawakan da suka rera ta.

Waƙar "We are the World" dai kamar yadda aka sani, waka ce da wasu mashahuran mawakan zamani na duniya, musanman Amurka suka rera ta a shekarar 1985 da nufin tara kuɗi domin taimakawa al'umar ƙasar Habasha dake fama da tsananin yunwa sakamakon farin da aka yi a ƙasar, wanda kuma yayi sanadiyar hasarar miliyoyin jama'a maza da mata da kuma kananan yara tsakanin shekarar 1984 zuwa 85.

Tarihi dai ya nuna cewar wani mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama Harry Belafonte ne ya fara tunanin kafa wata gidauniya da zata samar da kuɗi domin taimakawa al'umar dake fama da yunwa a ƙasar ta Habasha dake nahiyar afirka.

Wannan shawara ta Harry Belafonte ta samu karɓuwa daga sauran mawaka irin su Lionel Richie da Marigayi Micheal Jackson da Quincy Jones da kuma Stevie Wonder.

Sauran mawaƙan da suka rera wannan waƙa sun haɗa da Diana Ross da Kenny Rogers da kuma sauran yan uwan Micheal Jackson irin su Jackie da La Toya da Marlon da Randy da kuma Tito. Duka duka dai mawaƙa 43 ne suka rera wannan waƙa, wanda aka kammala ɗaukan sa a ranar 28 ga watan Fabrairun 1985. A yayinda kuma aka ƙaddamar da waƙar a ranar 7 ga watan Maris ta 1985.

Bayan da aka ƙaddamar da waƙen an dai tara zunzurutun kuɗi har Dala miliyan 63, a matsayin kuɗin taimakon jinƙai ga al'umar ta Habasha, kuma an saida faya fayan waƙar har miliyan 20. Bayan ƙasar ta habasha da aka baiwa wannan taimakon kuɗi, haka kuma akwai wasu ƙasashen na Afirka irin su Nijer da Burkina Faso da Mozambik da Senegal da Chadi da Mali da kuma Murtaniya da suma aka taimakawa da kuɗaɗen domin inganta aiyukan Noma da Kiwo da kuma kiwon Kifi da Inganta Ruwan Sha da Kare Gandun Daji. Waƙar ta samu kyautuka iri-iri na bajinta har guda uku da suka haɗa da Grammy da American Music Award da Peoples Choice Award.

A ƙarshe dai a sakamakon farin jinin da wannan waƙe yayi, ansha rera waƙar a guraren taruka da dama, walau dai na juyayi ko kuma murna. Kamar yadda aka rera waƙar a wajen juyayin mutuwar shahararren mawaƙin nan na zamani wanda ya rasu a bara wato Micheal Jackson.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal