Matsayin gwamnatin Mali a shari'ar Sanogo
December 2, 2013Ma'aikatar tsaron Mali ta ce ba za ta yi katsalanda ko kuma yin kafar ungulu ga shari'ar da za a yi wa tsohon shugaban mulkin sojin kasar Janar Amadou Sanogo ba.
Ministan tsaron na kasar Soumeylou Boubeye Maiga ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce zai tabbata ya bada tallafi don shari'ar ta gudana ba tare da wata matsala ba, kana ce zai kokarin ganin duk sojan da aka gayyata ya bada ba'asi ya je kotun don yin hakan.
Mr. Maiga ya kuma ce gwamnatin kasar ba ta da hannu wajen tsare Janar Sonogo da aka yi da ma dai gurfanarsa gaban kuliya, mutanen da aka yi wa ba daidai ba lokacin da Sonogon ke kan mulki ne suka nemi kotu ta bi musu kadi.
Ana dai tuhumar Janar Amadou Sonogo ne da bacewar wani hafsan sojin kasar da ma dai mutuwar wasu soji shidda lokacin wani bore da sojoji suka sa'ilin da ya ke jagogarantar kasar bayan juyin mulkin da ya yi cikin watan Maris din shekara ta 2012.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu-Waba