1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayar da aka cimma kan shirin nukiliyar Iran

January 13, 2014

Shugaban Amurka Barack Obama ya yaba da yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar Iran wanda kasashen yammancin duniya ke nuna damuwa a kai.

https://p.dw.com/p/1ApU5
Iran Uran Atomanlage
Hoto: Getty Images

A wani sako da ya aike wa kungiyar tarayyar Turai, Obama ya ce lokaci ya yi da za a yi amfani da hanyoyin na diflomasiyya wajen ganin an cimma wannan nasara da aka sanya a gaba. Sai dai a hannu guda ya ce Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kakaba wa Iran din wasu takunkumai muddin ta ki mutunta wannan yarjejeniya da aka cimma.

Daga cikin irin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa dai sun hada da sassauta gudanar da shirin Iran din na nukiliya da ma dai bai wa jami'an Majalisar Dinkin Duniya damar sanya idanu kan Iran din game da shirin nata, yayin da a gafe guda za a sassauta wa Iran din jerin takunkumin karya tattalin arzkin da aka kakaba mata.

Ana dai sa ran wannan yarjejeniya za ta fara aiki cikin 'yan kwanaki kalilan da ke tafe, kuma an kebe watanni shidda domin ganin yadda abubuwa za su wakana kafin a kai ga cimma wata yarjejeniyar ta dindidin.

To sai dai duk da cewar an kai ga wannan ci gaba, Iran din har yanzu na kan bakanta cewar shirin nata fa na zaman lafiya ne, hasali ma ta na yinsa ne da nufin samar da makashi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal