Matsalar yunwa a wasu kasashen duniya | Labarai | DW | 12.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar yunwa a wasu kasashen duniya

Hakan ya bayyana ne a rahoton shekara-shekara a kan yunwa, inda kididdigar ke cewa wasu yara na fiskantar barazanar tsumburewa

Duk da cigaban da aka samu wajen yaki da yunwa da karancin abinci a duniya, kungiyoyin bayar da agaji sun ce mutane milliyan 765 ne ke fama da karancin abinci mai gina jiki a rahoton shekara ta 2015 kan matsalar yunwa a duniya baki daya.Kididdigar dai ta kara nunar da cewa, kowanne yaro guda a cikin yara hudu na fiskantar hatsarin tsumbure ma sakamakon rashin abincin, sannan kuma kashi tara na duk yaran, rahsin abincin na hana su girma daidai da yanayin da ya kamata su kai a shekarun da suke. Yawanci dai rikice-rikice ne ke sanadin yunwan a wasu yankuna in ji rahoton.

Karancin abincin dai in ji wannan rahoto ya fi kamari a akasashen Afirka, a kasashen da suka hada da Chadi, da Zambia da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. To sai dai duk da wannan labari idan aka kwatanta da kididdigan da aka yi a shekara ta 2000 an sami cigaba na wajen kashi biyar. Kungiyoyin da cibiyoyin da suka gudanar da wannan binciken dai sun yi amfani da bayanai daga kasashe 117.