Matsalar yinwa a Tchad | Labarai | DW | 30.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar yinwa a Tchad

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta bayyana matsanacin halin ƙarancin abinci, da al´ummomin ƙasar Tchad, su kimanin dubu 130 ke fuskanta, a sanadiyar halin gudun hijira ,da su ka tsinci kan su a ciki.

Kakakin hukumar, Christiane Berthiaume ta ce dukkan wannan mutane, sun ƙaura daga gidajen su, a dalilin tashe-tashen hankulla a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Domin kawo tallafi ga wannan jama´a, hukumar na bukatar a ƙalla dalla milion 7 da rabi, ta fannin abinci barguna da magungunna.

Bayan mutanen Ƙasar Tchadin, hukumar na kai agaji ga ƙarin yan gudun hijira Sudan, kussan dubu 250, da ke tsugune a iyakar Tchadi.