Matsalar ′yan gudun hijira a Turai | Labarai | DW | 13.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar 'yan gudun hijira a Turai

Kawo yanzu dai wadannan mutanen suna cikin kwale-kwale anki barin su sauka, akasarinsu 'yan kasashen Afirka ne da aka hanawa ficewa bayan sun taso daga kasar Italiya

Hakan dai ya zo ne, bayan da suka shafe dare na biyu a bakin iyakar kasashen biyu. 'Yan gudun hijiran na ci-gaba da zanga-zanga ta lumana, tare da neman a basu hanya su fice domin shiga kasashen Turai, yayin da su kuma jandarmomi da ke bakin iyakar ta Vintimille suka ki basu hanyar ficewa.

Su dai 'yan gudun hijiran, sun kasance a bakin teku, inda kuma a nan ne suke wankansu, da sauran wasu bukatunsu, sannan kuma cikinsu akwai mata da yara kanana, inda a jikin kwalayen da ke hannunsu aka rubuta cewa muna son ficewa, ko kuma muna meman yancin walwala.

A kalla 'yan gudun hijira dubu 50 ne suka iso kasar Italiya daga farkon shekara kawo yanzu, amma kuma suna fiskantar matsalar samun ficewa zuwa kasashen na Turai.