1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD na neman agaji a yankin Sahel

Gazali Abdou Tasawa
January 17, 2022

MDD ta yi shelar neman agaji makuddan kudi domin fuskantar matsalar 'yan gudun hijira a kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/45e5d
Niger Diffa | Rückkehr von Flüchtlingen
Hoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Majalisar ta yi wannan kira ne a cikin wani rahoto da ta fitar wanda ya nunar da yadda adadin 'yan gudun hijira a yankin Sahel ya ninka sau 10 a cikin shekaru 10 a sakamakon hare-haren 'yan ta'adda wadanda suka kaddamar da farmaki sama da 800 a shekarar da ta gabata kadai a yankin. Tuni kuma kungiyoyin agaji na ciki da wajen kasar ta Nijar suka soma tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu.

A cikin rahoton da Hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR ta fitar a karshen mako, ta ce adadin mutanen da yakin da ake fama da shi a yankin na Sahel daga shekara ta 2013 zuwa karshen 2021 ya tilasta wa tserewa daga garuruwansu ya kai mutun miliyan biyu da dubu 100 wato ya ninka sau 10 a cikin kasa da shekaru 10.

TABLEAU | Weltflüchtlingstag 20.6.2021 Bildergalerie
Wasu 'yan gudun hijira a TripoliHoto: MAHMUD TURKIA/AFP via Getty Images

Sai dai rahoton ya ce matsalar ta fi kamari a kasashen tsakiyar yankin Sahel wato Mali da Nijar da Burkina Faso wadanda yawan mutanen da suka fice daga garuruwan nasu zuwa wasu yankunan na kasashensu ya kai mutun dubu 410 kana wasu dubu 36 sun ketara zuwa kasashe makwabta.

A jamhuriyar Nijar adadin 'yan gudun hijira na cikin gida a jihohin Tillabery da Tahoua ya karu da kaso 53 cikin 100 a watanni 12 da suka gabata. Ita ma dai kungiyar EPAD mai fafutikar kare hakkin yara da mata a Nijar ta bakin shugabanta Malam Sadikou Moussa nuna damuwa ya yi a game da halin da mata da yara suke ciki a tsakanin 'yan gudun hijirar a kasar ta Nijar.

Rahoton MDD ya ce ma'aikatan agaji na ci gaba da fuskantar kalubale wajen samun damar kai wa a matsugunnan 'yan gudun hijirar a sakamakon hare-haren da 'yan ta'addan ke ci gaba da kai musu saman hanya inda suke kwace musu motocin aiki. Sai dai Malam Djibo Halidou magajin garin Sarakoira fadar karamar hukumar ta Anzourou inda matsalar tsaron ta fi kamari, ya ce mutan gari da kungiyoyin agaji na ciki da na waje da ma gwamnati, ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kawo dauki ga 'yan gudun hijirar a yankin nasu;

Dandazon 'yan gudun hijira a Diffa, Nijar
Dandazon 'yan gudun hijira a Diffa, NijarHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Ya ce "An samar da wuraren zama kusan 248 ga 'yan gudun hijirar a garin Sarakoira fadar magajin garin yankin na Anzourou. A fannin taimakon kayan abinci da na bukatun yau da kullum ga 'yan gudun hijirar, nan ma mutanen gari da kungiyoyin kasa da kasa da ma gwamnati ba su yi kasa a gwiwa ba. Don ko a makon da ya gabata, shugaban kasa ya aiko mana da ton 100 na cimaka".

Sai dai rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce hukumar kula da 'yan gudun hijirar na bukatar tallafin kudi miliyan 307 na Dalar Amirka domin tunkarar wannan matsala ta 'yan gudun hijira a shekara ta 2022 a kasashen Burkina Faso da Nijar da Mali.