Matsalar tsaro ta tilasta wa fira ministan Chadi yin murabus | Labarai | DW | 21.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar tsaro ta tilasta wa fira ministan Chadi yin murabus

Majalisar ministocin Chadi ta yi murabus gabannin jefa mata ƙuri'ar rashin iya mulki.

Fira ministan kasar Chadi Joseph Djimrangar Dadnadji ya yi murabus tare da ɗaukacin ministocin gwamnatinsa. Wannan matakin ya zo ne yini ɗaya kacal gabannin majalisar dokokin ƙasar daga jam'iyyarsa ta gudanar da zaman nazarin ƙudirin da ya shafi yanke ƙauna daga iya mulki. 'Yan majalisa 74 ne suka sanya hannu a kan ƙudirin dokar, wanda suka gabatar wa majalisar dokoki da ke sukar salon mulkin fira ministan, dangane da gaza shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar ƙasar, da gaza shawo kan hau-hawan farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa. Dama dai fira ministan ya bayar da umarnin gudanar da garambawul ga majalisar ministocin har sau biyar cikin tsukin watanni 10. A cikin wasikar da ya gabatar wa shugaba Idris Deby Itno, fira minista Dadnadji ya ce bisa la'akari da irin hatsarin da ke tattare da makomar irin wannan ƙudirin ne, ya ɗauki matakin mika takardar yin murabus, tare da gwamnatin da yake jagoranta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdurahamane Hassane