Matsalar makiyaya da manoma a Najeriya | Siyasa | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar makiyaya da manoma a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen kawo karshen matsalar rikicin makiyaya da manoma tare da girke jami’an tsaro da za su kare gonaki da dabbobin makiyaya.

Flash-Galerie Tuareg (AP)

Manyan jami'ai da ke kula da harkokin tsaro a karkashin ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriyar sun bayyana takaici kan yadda aka kashe jama'a a rikicin makiyaya da manoma a jihar Benue da Taraba, abin da ke haifar da zaman tankiya tsakanin jama'a.

Wannan matsala ta kai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ganawa da gwamnan jihar ta Benue da kuma na baya-bayan nan gwamnan jihar Filato Simon Lalong a kokarin da ake na magance matsalolin tashe-tashen hankulla da ake samu a tsakanin kabilu makiyaya da manoma kaman yadda yake wakana a jihohin Taraba da Benue domin yi wa tubkar hanci.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin