Matsalar katsewar wutar lantarki a Kamaru | Zamantakewa | DW | 24.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalar katsewar wutar lantarki a Kamaru

Harkokin arzikin Kamaru na fama da tarin matsaloli a tashar ruwan Douala sakamakon karancin wutar lantarki. Lamarin da 'yan majalisa sun bukaci a gudanar da bincike a kai.

Daruruwan 'yan kasuwa ne dai a tashar ruwan Douala ke zaman jiran tsammani ko an kawo wutar lantarki don su sami damar fitar da kayyayyakinsu. Dan kamasho Muchi Awah ya ce akwai kimanin kwantena ta daukar kaya 2500 da masu su ke neman a basu dama su dau kayansu abin ya gagara sama da makwanni shida kenan, kayan kuma ana so ne a kaisu Chadi ko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ko wasu kasashe da ke kusa. Abin da ke jawo asara ga 'yan kasuwar. Awah ya ce " ana kara biyan kudin ajiyar kwantena a kowace rana saboda ba a dauka ba, sakamakon rashin wutar lantarki.

Shi kuwa Emmanuel Vermo da ke gyaran irin kwancen motoci da ake shigowa da su kafin su kama hanya zuwa wasu kasashe ya ce shi kan wannan matsala ta karancin wutar lantarki ta sanya ma ya na neman rasa sana'arsa. Vermo ya ce " mun samu kai cikin wani hali, bamu san me za muyi ba da na'urorinmu na aiki da ke bukatar wuta. Yaushe ne za a kawo wutar sannan yaushe ne kuma babu, hakan ya sanya ba ma iya hasashe kwanaki nawa za mu yi mu gudanar da wani aiki a kasuwancinmu."

Dan majalisa Walang Richard ya ce bayan yawan korafe-korafe da ya ke sha daga al'ummar da yake wakilta a majalisar dokokin kasar ta Kamaru, ya matsa kaimi wajen jan hankalin takwarorin aikinsa a gudanar da binciken kan musabbabin abin da ke jawo rashin tsayawar na wutar lantarki. Honorable Walang ya nunar rashin wutar da barazana ga makomar jarrabawar dalibai inda ya ce " yara da ke karatu za su zana jarrabawa amma kuma an dauke wuta. A ina za ka ga kyandir da misalin karfe daya biyu ko uku na dare"

Kasar ta Kamaru dai na bukatar a samar da Megawatt 12,000 na wutar. Amma sai Megawatt 721 ne ke samu a halin yanzu, abin da wasu 'yan majalisar ke ganin laifi ne na kamfanin Birtaniya da ke samar da wutar a Kamaru ENEO. Su kuwa mahukunta a kamfanin na ganin matsala ce ta rashin samun ruwan sama da zai motsa na'urori da suke da su.