Matsalar fataucin yara a Afirka | Learning by Ear | DW | 30.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Matsalar fataucin yara a Afirka

A karon farko da fara shirin ilimantarwa na "Ji ka ƙaru" tashar DW ta yi nunin wasan kwaikwayo a Lome na labarin da ya lashe gasar kacici kacicin da aka shirya bana.

Wannan labari da Bouloufei Bewezima ɗan asalin Togon ya tsara, ya na bayani ne kan fataucin yara ƙanana da kuma sanya su aikin da ya fi ƙarfin shekarunsu.

Farin ciki da annashuwa mazauna ƙauyen su Malick suka nuna a cikin wannan labarin, lokacin da shi da 'yan uwansa da kuma Pemba suka dawo garinsu na asali. Dalili kuwa shi ne: sun shafe watannin shida suna aikin da ya fi karfin shakarunsu a kasar waje ba tare da suna so ba.

Gwaggon su waɗanda yara ta yi alkawarin ba su kulawa da tarbiyar da suka dace lokacin da ta ɗaukosu a gaban iyayensu. Sai dai maimakon sa Malik da Pemba a makaranta, tura su kasar waje ta yi inda aka tilasta musu aikin dole a gida da kuma gonar wani hamshakin manomi. Amma kuma duk da takaici da talakawansa ke nunawa dagacin garin su Malik ya nemi karin haske daga gwaggon wadannan yara.

'Yan wasa 35 galibinsu yara ne suka bayar da gudunmwa wajen hada wasan na kwaikwayo da ya zo na daya a gasar a gasar " Ji ka karu" na DW. Wannan dai shi ne karon farko da wasu daga cikinsu suka taba wasan kwaikwayo ciki kuwa har da Méschak Gnaro mai shekaru 11 da haihuwa.

"Wannan dai ya burge ni sosai musamman ma kasance da Malik da ya karamin kwarin guywa na yi wasan. Lokacin da na tafka kura kurai, ya yi ta ba ni shawarwari da suka taimakin min magance matsalolin da na fiskanta. Da farko dai na dan ji tsoro saboda na za a yi cikan kwari. Mutane su halarci wasan kwakwayon sosai, amma kuma ban tsorata ba."

Kafin dai su yi wasan a cibiyar yada al'adun Jamus da ke birnin Lome, Méschak da sauran 'yan wasan na kwaikwayo sun shafe mako guda suna nazari a kowani la'asar. Da ma dai nakaltar da matasa dokoki wasan kaikaiyo na daya daga cikin fannoni da gasar kacici kacici na "Ji ka karu" na Dw ya tanada. Masu saurare daga sassa dana daban na Afirka ne suka aiko da labaransu masu ban sha'awa da ilimantarwa, da za su taimaka wa matasa tsara rayuwarsu don gaba. Bouloufei Bewezima na kungiyar "A nous la Planete " ne zo na daya. Tun da farko dai ya gina labarin na sa ne ta yadda mutane ba za su kosa ba lokacin da suke kallon wasan na kaikayo.

Imammcule Nyonhue na rera waka ne domin bayyana farin cikinta dangane da dawowan 'yayanta Malik da 'yan uwansa lami lafiya. 'Yar wasar kwaikwayon ta ce ta wannan hanye ce za a iya jawo hankali ga kaurace wa dabi'ar sa yara aikin da ya fi karfin shekarunsu.

"Wannan wasan kaikayo abin a yaba ne .Ni dai ya burge ni domin ya na tsokaci ne kan farautar yara da sanyasu aikin karfi. Wannan matsala ce da ke ci mana tuwo a kwarya anan Togo. Ina ganin cewar wannan zai fadarkar da jama'a, ya kuma tabbatar da musu da cewa yara na hakki."

Yaki da sa yara aikin karfi ba wani sabon abu ba ne tsakanin 'yan wasan na kwaikayo, saboda a matsayinsu na mamba a kungiyar " A nous la Planete" sun saba taruwa domin nazarin hanyoyin da za su dakile sa yara ƙanana aikin ƙarfi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita : Zainab Mohammed Abubakar