1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure na kara kwarara zuwa neman mafaka a Turai

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 25, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla bakin haure 3,000 ne ake sa ran za su rinka tsallakawa zuwa Macedonia a kowace rana cikin watanni masu zuwa.

https://p.dw.com/p/1GLI5
Yanayin da 'yan gududn hijira ke ciki a Macedonia
Yanayin da 'yan gududn hijira ke ciki a MacedoniaHoto: DW/N. Rujevic

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar UNHCR ce ta sanar da hakan, inda ta ce mafiya yawan bakin hauren 'yan gudun hijira ne da ke tserewa yakin kasar Siriya. Hukumar ta UNHCR ta kara da cewa ya zamo wajibi baki dayan kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU su kasafta 'yan gudun hijirar a tsakaninsu dai-dai wa dai-da duk kuwa da cewa a kan samu iyali guda da ke da yawan gaske wadanda ke neman mafaka a lokaci guda. A cewar hukumar akallah bakin haure 300,000 ne suka ketare Tekun Bahar Rum cikin wannan shekara inda 181,500 ke kasar Girka yayin da wasu 108,500 kuma ke Italiya kana wasu dubu 10,000 sun tsallaka zuwa Macedonia. Ta kara da cewa kaso 30 cikin 100 na 'yan gudun hijirar mata ne da kananan yara.