1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsa binciken gano Ebola a Amurka

Yusuf BalaOctober 11, 2014

Cikin matakan binciken har da wasu nau'in bindigogi da za su samar da bayanai hadi da takardun tambayoyi da ake bawa fasinjoji dan gano ko suna da Ebola.

https://p.dw.com/p/1DTZp
Gesundheits-Screening am Casablanca Flughafen in Marokko
Hoto: picture alliance/AP Images/A. Bounhar

A ranar Asabar dinnan ake fara gudanar da wannan aikin bincike, a filin tashi da saukar jiragen sama na John F.Kennedy da ke zama na farko cikin manyan filayen tashi da saukar jiragen sama biyar na Amurkan dan gudanar da binciken kwakwaf daga matafiya, da ke shiga kasar daga kasashen Laberiya da Guinea da Saliyo wadanda wannan annoba tafi yi wa barna inda tuni ta hallaka mutane sama da dubu hudu.

Kusan dai mafi akasarin fasinjojin da kan shiga Amurkan daga wadannan kasashe kan shiga ne ta filayen tashi da saukar jiragen saman na John F.Kennedy da Newwark Liberty da Washington Dulles da Chicago O'Hare da Hartsfield-Jackson Atlanta wadanda suma za a fara gudanar da irin wannan bincike a mako me kamawa.

A cewar cibiyar da ke da alhakin lura da kare aukuwar bazuwar cutittikan ta CDC, wannan bincike na zama wani bangare na tsare-tsaren Amurkan wajen yaki da wannan annoba ta Ebola.