Matashi mai sana′ar walda a Bauchi | Himma dai Matasa | DW | 03.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi mai sana'ar walda a Bauchi

"Sana'ar walda ta fi min aikin gwamnati don bana ji akwai aikin da zai ba ni salari da ya wuce abin da nake samu a wannan sana'a." A cewar Nasir Muhammad Lawal.

Mafi akasarin matasa wadanda suka yi karatun zamani mai zurfi musamman a arewacin Najeriya sun fi raja'a ne ga dogaro da aikin gwamnati, sai dai kuma kamar yadda Bahaushe ke fadi ba duka ne ake taruwa a zama daya ba kamar yadda wani matashi a jihar Bauchin Najeriya da ya kammala karatunsa a jami'a sannan kuma bai samu aiki ba ya kama sana'ar walda.

Matashin mai suna Nasir Muhammad Lawal ya bayyana wa DW cewa ya shafe tsawon shekaru yana neman aiki tun bayan da ya gama karatunsa amma kuma bai yi nasarar samun aikin ba. Lura da cewa yawancin wadanda suka yi karatu ba su cika yin sana'a ba, ko shin me ya sa Nasiru ya ji ya fara wannan sana'a ta walda?

Bana so na zama cima zaune a cikin al'umma, kuma wannan sana'a ta yi min komai na yi aure mutane da dama na dogara a karkashina.

Schweisser (AP)

To amma ko me ya ja hankalin Nasir ya zabi wannan sana'a ta walda duk da yake ba bangaren da ya a karanta ba kenan a jami'a? " E wannan sana a ita na fi sha'awa kuma abin da nake samu ko da aikin gwamnati nake yi ba lallai ya ba ni kudin da nake samu ba."

Idan Nasir Muhammad Lawal ya samu aikin gwamnati, shin zai iya barin wannan sana'a ta walda kacokam? "A a ba zai yi yiwu ba idan ma aikin zai hana ni wannan sana'a ina iya ajiye shi."

Nasir ya bayyana cewa akwai matasa da dama da suke koyon wannan sana'a ta walda a shagonsa, wadanda kuma su ma suna zuwa makaranta sannan kuma idan sun dawo su zo shago.

Sauti da bidiyo akan labarin