Matashi mai inganta noma | Himma dai Matasa | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi mai inganta noma

Wani kwararren Manomi a Najeriya na horar da matasa hanyoyin zama manoman zamani daga na gargajiya ta hanyar rungumar noma da machinan da ake anfani da dabbobi zuwa na zamani dan wadata kasa da abinci.

Domin chanza fasali da tsarin Noma daga na gargajiya zuwa na zamani, da kuma tabbatar da ganin cewa an rage tilastawa dabbobin shan magunguna da ke cutar da su wajan huda, tare kuma shigowar wasu sabbin fasahohi da kirkire-kirkiren da suka jibanci na inganta harkar noma  su ne dai dalilan da suka sanya wannan manomin kaddamar da wannan kamfe irin san a farko a Nigeria domin dai wayar da kan Matasa da Magidanta Manoma sabbin dabaru da hanyoyin zama kwarrarun manoman zamani dan tafiya da noman zamani Domin yaki da karancin abunci ko tsadar sa a Najeriya.

Malam Abdulrahman Ali musa shi ne dai shugaban wata kungiyar da ke fafatukar ganin dukkanin ‘yan Nigeria sun koma Gona(back to land NGO) yace abun da ya sanya muka shiga shirin na ilmantar da manoma sabbin dabarun Noma na zamani shine,don chana fasalin Noman daga na gargajiya zuwa na zamani don wadata kasa da abunci,tare kuma da fargar da manoman gargajiya sabbin dabaru da fasahohin Noma da duniya ke anfani da su,wajan yaki da karancin abunci a Duniya

Malam Abdulrahman yace mun lura cewa Dayawa daga cikin manoman karkara a tarayar Nigeria,suna anfani da tsaffin hanyoyin noma na gargajiya da kuma yadda suke cin zarafin dabbobin su ta hanyar basu miyagun magungunan da ke cutar da su wanda ke da hatsarin gaske ga rayuwar dabbobin,da kuma janyo hankalin su akan Noma manyan filayen Noma,maimakon kananan filayen da suke anfani da su wajan Noma da suka gada tun daga kakanni-da-kakanni.