Matar Mugabe ta koma gida | Labarai | DW | 20.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matar Mugabe ta koma gida

Uwar gidan shugaban kasar Zimbabuwe Grace Mugabe ta koma gida a wannan Lahadin daga kasar Afirka ta Kudu bayan zarginta da cin mutuncin wata matashiya 'yar shekaru 20 a wani Otel da ke birnin Johannesburg.

Uwar gidan shugaban kasar Zimbabuwe Grace Mugabe ta koma gida a wannan Lahadin daga kasar Afirka ta Kudu bayan zarginta da cin mutuncin wata matashiya 'yar shekaru 20 a wani Otel da ke birnin Johannesburg. Da fari dai 'yan sandan Afirka ta Kudu sun rufe dukkanin iyakokin kasar don hana Grace Mugabe ficewa daga kasar, sai dai wasu rahotannin sun ce madam Grace Mugabe ta sami kariya ta diplomasiyya.

Kafofin watsa labaran kasar Zimbabuwe a wannan Lahadin, sun tabbatar da komawarta Harare babban birnin kasar tare da mijinta Robert Mugabe, kamar yadda shi ma kamfanin dillancin labaran Reuters, ya labarta. Matashiyar Gabriella Engels, ta zargin matar Mugaben ne 'yar shekaru 52 da dukanta da wayar lantarki da ya kaiga yi mata rauni a goshi, lokacin da ta ke zaman jiran daya daga cikin 'ya'yan Mugabe a Otel din.