1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Kamaru sun shiga yajin cin abinci

Abdul-raheem Hassan
May 21, 2021

Dubban mata a Kamaru sun shiga yajin cin abinci don jan hankalin manyan kasashen duniya kawo musu dauki kan rikicin yankin da ke magana da Turancin Ingilishi da ya halaka rayuka da dama. 

https://p.dw.com/p/3tnEO
Kamerun - Markt in Yaounde
Hoto: picture-alliance/Bildagentur-online/AGF

Matan dai sun gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kamaru da zummar matsa wa gwamnati samo mafita kan rikicin yankin masu magana da turancin Ingilishi a kasar. Sai dai yunkurin ya gaza yin nasara, wannan ya sa matan suka sauya salo, dubbai daga cikinsu sun ja daga na shiga yajin cin abinci har sai hakarsu ta cimma ruwa.

“Na tashi ba tare da cin komai ba. Yanzu haka ina jin wani iri, saboda tsananin yunwa. Bugu da kari kuma ina ramewa saboda na dau kwanaki ba na cin abinci a cewar wata matar da ke yajin cin abinci”

Duk da irin wannan radadi, matan sun ce ba gudu ba ja da baya, a cewarsu, za su ci gaba da zama da yunwa har sai bukatarsu ta biya, samar da mafita kan rikicin. Farida Baye Ebai, ita ce ja gaba.

“Ba za mu janye ba yanzu. Ba kuma za mu saurara ba. Za mu cigaba da yajin cin abinci. Kuma muna kira ga sauran mata su bi sahunmu. Gwagwarmaya ce ta kai da kai, ba mu tilasta kowa.”

To sai dai baya ga neman kawar da rikicin yankin Ambazoniya, akwai tarin matsaloli da ke damun matan kamar fyade, kisan gilla da kuma garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

”A matsayin mata, mu ne ke jin radadin rashin 'ya'ya. Na rasa yara dalilin wannan rikicin, na rasa 'yan uwa, mu ke jin zafin haihuwa, mu ne kuma ke ji da wahalar kula da yara. Wannan ya sa muke wannan tafiya ta shiga yajin cin abinci.

Gwamnatin Shugaba Joe Biden na Amirka ta nuna alamun sa baki a maganar, inda sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya ce lokaci ya yi da Washington za taka rawa a rikicin na Kamaru. Yanzu haka dai kusan shekaru biyar kenan ake gwabzawa, sai dai an yi hasarar rayukan mutane akalla 3,500 yayin da wasu mutanen sama da miliyan daya suka yi gudun hijira.