Matakin Sarkin Gombe na bunkasa ilimi | Himma dai Matasa | DW | 31.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matakin Sarkin Gombe na bunkasa ilimi

A Najeriya Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar III ya dukufa wajen taimakon yara marasa galihu da kuma bunkasa ilimi.

Yayin ake cigaba da kokawa kan yadda sha'anin ilimi ke cigaba lalacewa a arewacin Najeriya idan aka kwatanta shi da kudancin kasar, Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar III ya dauki gabarar sanya yara makaranta domin ganin an ilimantar da yara a jihar.

Irin gararambara da yara ke yi a kan tituna sakamakon rashin zuwa makaranta wanda hakan ke da nasaba da maraici ko ma rashin karfi daga bangarenm iyaye na daga cikin abinda ya sanya Sarkin na Gombe yanke shawarar ba da gudumawarsa wajen ganin an ilimantar da yara a Jihar Gomb.

Domin ganin cewar na samu dorewar wannan shiri na ilimantar da yaran da Sarkin na Gombe ke daukar dawainiyarsa, a zantawarmu da shi ya bayyana irin matakan da ya dauka don ganin kwalliya ta kai ga biyan kudin sabulu.

To baya ga batun ilimi na Firamare wanda Sarkin na Gombe Abubakar Shehu ya dukufa wajen baiwa yara, ya kuma bayyana cewar zai cigaba da dauakr dawainiyar daliban a makarantun gaba da firamare da ma abinda ya fi haka.

Tuni dai masana harkokin ilimi suka fata tofa albarkacin bakunansu kan wannan hiobbasa din da Sarkin ya yi har ma wasunsu suke kira ga takwarorinsa da masu hannu da shuni kan su yi koyi da shi. Su kuwa yaran da ke cin moriyar wannan shiri godiyarsu suka mika ga Sarkin.