Matakan saka ido kan harkokin makamai a Amirka | Labarai | DW | 05.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan saka ido kan harkokin makamai a Amirka

Fadar shugaban Amirka ta gabatar da jerin matakai da za su taimaka wajen kara saka ido ga amfani da makamai a kasar a wani mataki na takaita kashe-kashen da ake fuskanta.

Barack Obama

Barack Obama

Wannan tsari zai tilastawa mafi yawan masu sayar da bindigogi samun takardar izini, yayin da su kuma masu saye za a kara zurfafa bincike a kansu. Yayin da yake magana a gaban 'yan jarida, Shugaba Barack Obama ya ce wannan tsari da fadarsa ta fitar na biyayya ga kundin tsarin mulkin Amirka, da kuma sashe na biyu da ke bai wa 'yan kasar izinin rike makamai.

A wannan Talata ce dai ake sa ran shugaban na Amirka zai ba da karin haske kan wannan mataki yayin wani jawabi da zai yi da yammaci.