Matakan farfado da tattalin arzikin Faransa | Labarai | DW | 08.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan farfado da tattalin arzikin Faransa

Sabon Firaministan Faransa Manuel Valls ya ce gwamatinsa za ta rage haraji da kudaden da ta ke batarwa a wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin kasar da ke da matsala.

default

Sabon firaministan Faransa Manuel Valls

Mr. Valls ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko a zauren majalisar ministocin kasar, inda ya ce daga cikin bangarorin da gwamnati za ta rage kudadaden da ta ke batarwa har da bangaren inshorar lafiya da kuma kananan hukumomi.

Kudaden da za a yi tsuminsu daga bangarorin da za a rage kashe kudin gwamnati inji firaministan za a karkatasu ne ga wasu bangarori don karawa tattalin arzikin kasar tagomashi.

Har wa yau, ya kuma ce gwamnatinsa za ta dafawa kamfanoni masu zaman kansu a wani mataki na ganin sun samar da aiyyukan yi ga 'yan kasar domin kaiwa ga rage yawan masu zaman kashe wando.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu