Matakan CIA na yiwa fursinoni tambayoyi | Siyasa | DW | 25.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matakan CIA na yiwa fursinoni tambayoyi

A ranar Talata ne aka gabatar da rahoton hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA a game da matakanta na rashin imani wajen fuskantar fursinoni da tambayoyi.

default

Babban atonin Amirka Eric Holder

Daga cikin waɗannan matakai har da barazanar kisan kai da fyaɗe da halaka 'ya'ya ko mata da uwayen fursinonin da lamarin ya shafa. Tuni dai ma'aikatar shari'a ta ƙasar Amurka ta ba da umarnin binciken lamarin dalla-dalla.

"Har abada ba zamu ɗauki wani matakin da ka iya zama barazana ga makomar tsaron lafiyar Amurkawa akan hukumar CIA ba. Ba zamu sa ƙafa mu yi fatali da al'amuran tsaron ƙasa ba."

Wannan bayanin an sha jinsa ne daga bakin ministan shari'a na Amurka Eric Holder. Amma kuma duk da haka bisa ga ra'ayin ministan shari'ar, fafutukar tabbatar da tsaron Amurka, ba ta isa ta zama hujjar ta'asar da mahukuntan CIA suka caɓa wajen fuskantar fursinoni da tambayoyi a zamanin mulkin shugaba Bush ba. An tara bayanai a game da waɗannan munanan matakai na fuskantar fursinoni da tambayoyi a cikin wani rahoto na asiri da inspekta-janar na CIA ya tanada a shekara ta 2004, wanda a yanzu aka gabatar da wani ɓangare daga cikinsa a takardar ƙarar da ƙungiyar kare haƙƙin farar fula ta Amurka ACLU ta gabatar ya kuma mamaye kanun labaran illahirin kafofin yaɗa labaran Amurka.

"Wani jami'in hukumar leƙen asirin Amurka CIA yayi barazanar kashe 'ya'yan Khalid Sheikh Muhammed, dake da hannu a hare-haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001, muddin aka sake kai wasu sabbin hare-haren ta'addanci a Amurka kamar yadda tashar CNN ta ambata daga rahoton. Shi kuwa ɗaya fursunan hukumar CIA barazana tayi game da yi wa mahaifiyarsa fyaɗe akan idonsa."

Rahotanni masu nasaba da jaridar New York Times wannan maganar ta shafi fursinoni ne da dama da aka tsare a Irak da Afghanistan tare da gallaza musu a ƙarƙashin hukumar CIA. Akwai ma rahotannin mace-mace dangane da wasu ɗaiɗaikun fursinonin. Kazalika akan yi musu barazanar kisa da kan bindiga ko huje kan fursina da injin. A lokacin da yake wa abokan aikinsa bayani, ministan shari'ar Amurka Eric Holder ya nuna kaɗuwa matuƙa ainun a game da waɗannan matakai na rashin imani. Tuni dai shugaba Barak Obama na Amurka yayi barazanar ƙayyade cikakken ikon da hukumar CIA ke da shi na fuskantar fursinonin da ake tuhumarsu da kasancewa 'yan ta'adda da tambayoyi. A maimakon haka nan gaba za a danƙa alhakin ne ga wata tawaga ta musamman da za a naɗa daga kafofin leƙen asirin dabam-dabam. Kuma Obama kansa na da shirin neman cikakken bayani daga majalisar tsaron ƙasa a game da matakan na CIA, in ji wani mai magana da yawunsa a fadar mulki ta White House.

Ya ce:"Shugaban na so ne tun daga yanzu ya mayar da hankalinsa wajen yin gyara nan gaba, amma ba waiwayar baya a game da ta'asar CIA da shugaba Bush ba. Obama ya sha yin bayani game da haka."

Mawallafa: Ralph Sina/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal