Babban alkali a kasar Masar, ya rantsar da mata 98 a matsayin lauyoyin gwamnati a karon farko bayan da matan suka sha yin zargin nuna musu wariya.
An rantsar da matan su kusan 100 a birnin Alkahira watanni kadan bayan da Shugaban kasar Abdel Fattah el-Sissi ya kirayi mata su shiga rukunin lauyoyin kare gwamnati.
A shekarar 1946, aka kafa hukumar shari'a mai zaman kanta da ke kula da rigingimun tare da yin bitar daftarin dokoki da yanke shawara da kwangilolin da suka shafi gwamnati.