1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Bore kan kuncin rayuwa a Yemen

Ramatu Garba Baba
March 16, 2021

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka afka cikin ginin gwamnati don jan hankalin hukumomi a game da kuncin rayuwar da jama'a ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/3qhON
Jemen l Explosion am Flughafen in Aden
Hoto: Al Arabiya/Reuters TV

Masu zanga-zanga a kasar ta Yemen sun afka wa wani katafaren ginin gwamnati da ke Aden babban birnin kasar. Daruruwan masu zanga-zanga na son ganin gwamnati ta dauki matakin inganta rayuwar jama'ar da ke fuskantar wahalhalu a sakamakon durkushewar duk wasu abubuwa na more rayuwa.

Rahotannin daga kasar na cewa, jami'an tsaro na kokarin shawo kan hatsaniyar da ake ganin, tura ce ta kai bango ga al'ummar da ke cikin tsanani na rashin ruwan sha da karancin abinci baya ga katsewar wutan lantarki a akasarin sassan kasar. Shekaru shida kenan tun bayan da Yemen ta tsinci kai cikin yakin basasa a sakamakon rikicin gwamnati da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.