Masu zanga-zanga a Masar na nuna turjiya
August 12, 2013Tsugune ba ta ƙare ba a taƙaddamar ikon da ke afkuwa tsakanin gwamnatin riƙon ƙwaryar Masar da magoya bayan hamɓararren shugaban ƙasar Muhammad Mursi.
A yau ma magoya bayan tsohon shugaban sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a duk faɗin ƙasar domin nuna adawa da shirin da gwamnati ke yi, na zuwa ta fatattaki waɗanda ke zaman dirshen a sansanonin da suka girka a babban birnin ƙasar wato Alƙahira.
Da bayyana wannan shiri na gwamnati, magoya bayan Mursin suka fara gina shingaye suna killace kansu a matsayin martaninsu ga barazanar da gwamnatin riƙon da Jami'an tsaron ƙasar suka yi.
A wani abin da ke nuna cewa barazanar ba ta ma yi tasiri ba, sansanonin sun ci gaba da samun ƙarin jama'a kamar ma ba su sami wannan sanarwa ba.
To sai dai ba a bayyane ya ke ba, ko a tsakanin 'yan kwanaki masu zuwa jami'an tsaro za su kara da magoya bayan Mursin.
Masu sanya ido dai na fargabar ta'azarar lamura, kasancewar masu zanga-zangar ko ɗaya ba su nuna alamar miƙa wuya ba, kuma sun haƙiƙance kan maida Mursi a matsayin shugaban ƙasa, zun bayan da aka tsige shi ran uku ga watan Yuli.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh