Masu yunkurin kai hari Burtaniya sun amsa laifunsu | Labarai | DW | 10.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu yunkurin kai hari Burtaniya sun amsa laifunsu

Wasu mutane biyu da ake zargi da kitsa wasu hare-hare a Burtaniya da sunan kungiyar nan ta Al-Qaida sun amsa laifunsu.

Mutanen biyu dai wato Mohammed Rizan da Bahader Ali sun ce shakka babu su na da hannu dumu-dumu a cikin harin da aka shirya kaiwa Birmingham, birni na biyu mafi girma a Burtaniya, wanda da sun samu nasarar kamar yadda masu gabatar da kara su shaida zai iya fin wanda aka kai cikin shekara ta 2005 muni.

Masu gabatar da karar dai sun ce mutanen da su ka amsa laifin sun yi yunkurin tada bama-bamai ne a wasu jakunkuna da su ka boye.

A cikin watan gobe ne idan Allah ya kaimu ake sa ran kotu za ta bayyana irin hukunci da aka yankewa mutanen. Idan dai ba a manta ba, a farkon wannan shekarar ce dai aka yankewa abokan huldar wadannan mutanen biyu su shidda hukunci.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu