Masu yawon bude ido sun tsallake hari a Masar | Labarai | DW | 19.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu yawon bude ido sun tsallake hari a Masar

An kai harin bam kan masu yawon shakatawa a kasar Masar yayin da suke tafiya a cikin motar safa, amma sun tsallake rijiya da baya.

Wasu masu yawon bude ido a kasar Masar sun tsallaka rijiya da baya, bayan da suka tsira daga wani harin da aka ka, mutune 17 da ke cikin motar safa sun sami raunika bayan da wani bam ya daki motar da suke tafiya a ciki.

An dauki matakin killace yankin da ke daf da dalar "Pyramid" bayan kwashe wadanda suka ji raunin. An gano akasarinsu sun fito ne daga kasar Afirka ta Kudu kamar yadda wani jami'in tsaron kasar ta Masar ya tabbatar. 

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watannin shida da ake yunkurin kai hari kan masu yawon bude ido a birnin na Alkhahira da jama'a musanman daga kasashen waje ke yawan tururuwa, a harin na can baya, wasu 'yan Vietnam uku ne suka rasa rayukansu.