1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu sanya ido a zabe sun yaba da zaben Ukraine

Mohammad Nasiru Awal ZMA
April 1, 2019

Sai dai duk da haka tawagar kungiyar OSCE da ta sa ido a zaben na Ukraine ta ce an yi amfani da kafafan gwamnati ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/3G3FH
Ukraine Präsidentschaftswahl 2019 | Iikka Kanerva, OSZE
Shugaban tawagar OSCE, Iikka Kanerva da suka sa ido a zaben UkraineHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Grits

Masu sa ido a zabe na kungiyar tsaro da hadin kai a Turai wato OSCE sun yaba da yadda zaben shugaban kasa ya gudana a kasar Ukraine, suna masu cewa an yi wa kowa adalci.

Sai dai duk da haka shugaban tawagar kungiyar ta OSCE da suka sa ido a zaben na Ukraine Iikka Kanerva ya ce an yi amfani da kafafan gwamnati ba bisa ka'ida ba an kuma saye kuri'u abin da ya dakushe sahihancin shirye-shiryen zaben da yanzu za a tafi zagaye na biyu.

"An yi gogayya a zaben shugaban kasar Ukraine. Masu kada kuri'a sun samu sukunin zaban abin da suke so, sun kuma fito kwansu da kwarkwatansu. Zaben ya gudana lamin lafiya, abin da ya bude hanyar zuwa zagaye na biyu. Sai dai a lokutan da suka gabaci zaben an yi wasu abubuwa da suka saba wa doka, da ya rage yardar da ake wa hukumar zabe."

Sakamakon zaben ya nuna cewa dan wasan kwaikwayo Volodymyr Zelenskiy ya ci zagayen farko da kashi 30 cikin 100, shi kuma shugaba mai ci Petro Poroschenko ya samu kashi 16 ckin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

A ranar 21 ga watan nan na Afrilu mutane biyu za su fafata a zagaye na biyu na zaben.