1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu sa ido sun isa kasar Yemen

Yusuf Bala Nayaya
December 22, 2018

Masu sanya idanu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun isa Yemen a wannan rana ta Asabar domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Hodeida.

https://p.dw.com/p/3AXR7
UN Sicherheitsrat Yemen
Hoto: Reuters/C. Allegri

Tawagar wacce ta samu jagoranci na Patrick Cammaert janar din soja mai ritaya daga kasar Holand ta fara sauka a birnin Aden inda halastacciyar gwamnatin da al'ummomin kasa da kasa suka amince da ita take.

A cewar jami'an gwamnatin kasar ta Yemen a birnin Aden Cammaert zai gana da shugabanni kafin daga bisani ya kama hanya zuwa birnin Sanaa babban birnin kasar inda 'yan tawaye suke kana daga bisani ya kama hanya zuwa birnin Hodeida.

Wannan dai na zuwa kwana guda bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura jami'ai masu sanya idanu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a kasar Sweden a kokarin samun zaman lafiya a kasar ta Yemen.