Masu maganin gargajiya da cutar Ebola | Siyasa | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Masu maganin gargajiya da cutar Ebola

Masu bayar da magungunan gargajiya sun gargadi takwarorinsu da su guji hulda da wadanda ke da cutar Ebola su shawarce su, su nemi magungunan da suka dace.

Garin Logan da ke daga waje-wajen birinin Monroviya, Liberiya, na daya daga cikin garuruwan da ke fama da cutar, haka nan kuma gari ne da al'ummarsa ta yi imani da magungunan gargajiya, inda wasu daga kabilun Liberiyan na asali ke da cibiyoyi, kaman wani wanda ake kira Dr Peace Centre for Alternative Therapy.

Wannan cibiya wanda ke bayar da magungunan gargajiya na karkashin jagorancin Peace Bello wanda ya shahara wajen baiwa mutane magugunan gargajiya wadanda ya ke samu daga cikin kasarsa ta Liberiya. To sai dai da aka yi masa tambayar yadda ya ke baiwa masu dauke da cutar Ebola kulawa, bai yi wata-wata ba wajen fayyacewa.

"Babu wanda ya taba zuwa waje na da cutar Ebola, duk cikin wadanda na ke dubawa babu mai dauke da wannan cuta, ba na bayar da maganin Ebola, babu abin da ya hada ni da wani mai dauke da Ebola".

Guinea Konacry Ebola Virus

Fadakarwa kann Ebola a kasar Guinea

Kasar Guinea na yaki da masu magungunan gargajiya

A yankin yammacin Afirkan dai kasar Guinea ma ta yi kaurin suna dangane da yaduwar wannan cutar ta Ebola, kuma su ma 'yan kasar sun yi ammana da amfani da magungunan gargajiya amma ba da dadewa ba, aka fara tababan sahihanci masu bayar da irin wadannan magungunan musamman da zuwan wannan cutar ta Ebola. Hasali ma a halin da ake ciki yanzu a Guinean yaki ma ake yi da wadanda ke ikirarin bayar da magungunan na gargajiya. Dr Sakoba Keita shi ne shugaban kula da hukumar bayar da kariya ga cututtukan da ke da saurin yaduwa

A yanzu, akwai batutuwa da yawa da ke cewa akwai masu magungunan gargajiya da suke gano maganin wannan cuta amma har yanzu babu hujjar cewa sun yi hakan

Ranar juma'ar da ta gabata, ministocin lafiya na kasashe hudu na kogin Mano wadanda suka hada da Côte d'Ivoire da Guinea da Liberiya da Saliyo suka gana a Guinea Conakry domin daukan matakan yaki da wannan cutar ta Ebola.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammad Awal Nasiru

Sauti da bidiyo akan labarin