Masu horaswa na gida a gasar AFCON
A karon farko cikin tarihin gasar cin kofin Afrika, masu horas da 'yaan wasa 15 cikin 24 sun fito daga nahiyar. Daga cikinsu akwai tsofaffin 'yan wasa da suka yi suna da kuma wasu masu horaswa na kasashen Afirkan.
Aliou Cissé - Senegal
Tsohon dan wasan baya mai farin jini ya yi nasarar sauya sheka zuwa horarwa. Tun bayan da ya karbi ragamar 'yan wasan Senegal a 2015, ya jagoranci kungiyar Lions zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018 da kuma zuwa wasan karshe na gasar cin kofin AFCON na 2019, inda ta sha kashi a hannun Aljeriya. Bayan wannan rashin nasara, yana fatan lashe kofin nahiyar a wannan karon kuma yana da kwakkwarar tawaga.
Norman Mapeza - Zimbabuwe
Tsohon dan wasan tsakiya, wanda ya taka leda a Galatasaray da Ajax Cape Town, shi ne kocin Warriors a karo na hudu a rayuwarsa yana a matsayin koci na wucin gadi a yanzu. A Kamaru, Mapeza yana kokarin inganta martabar kwallon kafar Zimbabuwe. Kungiyar dai na halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka a karo na biyar a tarihinta, kuma karo na uku a jere.
Kamou Malo - Burkina Faso
Malo (a dama) wani jigo ne a cikin nasarorin da kungiyoyin kwallon kafa na Burkina Faso suka samu a cikin shekaru goma da suka gabata. Ya jagoranci kungiyoyi da dama a gasar cikin gida, kuma an nada shi kocin Etalons a watan Yulin 2019. Kazalika shi ne manajan kungiyoyin matasa na kasa a Burkina Faso.
Baciro Cande - Guinea-Bissau
Candé ya zama koci bayan ya shafe tsawon lokaci yana buga kwallo a Portugal. Ya horar da kungiyoyin cikin gida da dama a lig Guinea-Bissau, kuma ya lashe kofunan lig guda tara tare da Sporting Clube de Bissau. Bayan ya buga wasan farko tsakanin shekarar 2003 zuwa 2010, ya koma babbar tawagar kasar a shekarar 2016 kafin ya samu nasarar kai kasar a gasar AFCON ta bana.
Amir Abdou - Tsibirin Komoros
Abdou ya fara aikin horar da ‘yan wasan ne a shekarar 2012 tare da kulob din Golfech na Faransa kafin ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan kasar Komoros a shekarar 2014. Tuni dai ya shiga cikin tarihi bayan da ya jagoranci kasarsa zuwa gasar AFCON ta farko bayan kunnen doki da ta yi daTogo a farkon wannan shekarar. Yana fatan haifar da wani abin mamaki yayin gasar.
Juan Micha - Equatorial Guinea
Bayan ya zama kocin rikon kwarya a shekarar 2020 saboda raba gari da kocin Faransa Sebastien Miché, Juan Micha ya zama mai horar da babban tawagar Equatorial Guinea a shekarar 2021. Bayan 'yan kwanaki, ya samar wa kungiyar N'zalang National tikitin shigar AFCON sakamakon samun nasara a kan Tanzaniya. Duk da cewa Micha ya yi nasarar sanya kungiyarsa cikin gasar, amma ta zama dan hakin da aka raina.
Mondher Kebaier - Tunisiya
Tsohon dan wasan CA Bizertin ya horar da kulob din Tunisiya da dama, inda ya lashe gasar cin kofin Tunisiya da Bizertin a 2013. A shekarar 2019 ne aka nada Kebaier a matsayin kocin tawagar kasar. Har yanzu kungiyarsa na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar, amma za ta fara kokarin lashe gasar cin kofin Afrika karo na biyu bayan gasar da ta lashe a shekara ta 2004.
Wubetu Abate - Habasha
Abate yana da ingantaccen tarihin horarwa a kungiyoyin Habasha da dama. Ya zama kocin kasa a hukumance a watan Satumba na 2020 kuma ya sami nasarar samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka duk da munin yanayin siyasar kasarsa. Ya kuma samu ’yan wasa daga yankuna dabam-dabam na kasar domin su yi wasa tare.
Pedro Leitão Brito "Bubista" - Cape Verde
Bayan ya buga kwallo a matsayin sana'a, "Bubista" ya jagoranci kungiyoyi da dama a Cape Verde. A watan Janairun 2020, aka nada shi manajan kungiyar kwallon kafa ta kasa kuma ya halarci gasar cin kofin AFCON na biyu kacal a tarihin wannan tsibiri na Afirka.
John Keister - Saliyo
Ko da yake ya buga wasan kwallon kafa na kasa da kasa a Saliyo, amma an haifi Keister ne a Ingila kuma ya taka leda a kasar tsawon rayuwarsa. A shekarar 2017 ne aka nada shi kocin tawagar kasar, amma ya bar kujerarsa a lokacin da ake cikin tashin hankali inda FIFA ta dakatar da kasar. Ya dawo a 2020 don taimakawa wajen tabbatar da cancantar shiga kasar a karon farko a gasar AFCON tun 1996.
Augustine Eguavoen - Najeriya
An kira shi don maye gurbin Gernot Rohr na Jamus, Amma Augustine Eguavoen ya san Super Eagles sosai. Wannan dai shi ne karo na uku da tsohon dan wasan na Najeriya (wanda ya buga wasanni 49 tare da cin kwallo 1) ya samu kansa a matsayin kocin Najeriya. Dole ne tsohon mai tsaron baya ya nuna kwarewa da jajircewa don kai Super Eagles gaba gwargwadon iko a wannan AFCON.
Mohamed Magassouba- Mali
Babban mai tsara fasalin wasan kwallon kafa na kasar Mali, kuma babban manajan kungiyoyin wasanni na Mali ya yi nasara inda da dama suka gaza tun bayan karbar ragamar tawagar kasar a 2019. Ma'ana ya samar da wata kungiya mai karfi da ta yi wa jimillar na baya tazara. Sannan a karkashinsa, Mali na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya a Qatar, kuma manufarsa ita ce nasara a gasar AFCON.
Burhan Tia - Sudan
Tia ya kasance wanda ba a san shi ba a cikin masu horarwa a gasar AFCON. An nada shi a watan Disamba 2021 don maye gurbin Hubert Velud, amma Tia ya taba horar da kungiyoyi dabam-dabam a Sudan. Zai yi kokari cire wa kungiyarsa kitse a wuta a rukuni mai wahala wanda ya kunshi Najeriya, Masar da Guinea-Bissau.
Kaba Diawara - Guinea Conakry
Tsohon dan wasan na Guinea, wanda ya taka leda a kungiyoyin Faransa da dama da suka hada da Bordeaux da PSG, ya fara ne a matsayin mai ba da shawara bayan da ya daina kwallon kafa. Amma a watan Oktoban 2021, Diawara ya sami damar horarwa ta farko, inda ya maye gurbin tsohon dan wasan Faransa Didier Six a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta Guinea.
Djamel Belmadi - Aljeriya
Dan wasan da aka haifa a Faransa ya fara aikin horar da ‘yan wasan ne a 2010 a Qatar, inda ya horar da kungiyoyi biyu da babbar tawagar ‘yan wasan kasar. Daga nan ne aka bai wa tsohon dan wasan na Aljeriya mukamin aikin horarwa a kasarsa a watan Agustan 2018 kuma ya lashe gasar AFCON a shekarar 2019. Belmadji dai fitaccen dan wasa ne a kasar Aljeriya, inda ya kawo kwarewa da jajircewa.