1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu dauke da makamai sun addabi Libiya

November 17, 2013

Sabon rikicin ya sake ballewa a kasar Libiya tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai

https://p.dw.com/p/1AJ1r
Hoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

Wani sabon fada ya sake ballewa tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a birnin Tripoli na kasar Libiya.

Rikicin ya barke cikin daren wannan Asabar da ta gabata, yayin da aka yi musanyen wuta tsakanin tsaregu masu dauke da makamai na birnin Misrata da masu biyayya wa gwamnati. Lamarin ya samo asali da mutuwar kimanin 43 sakamakon tashin hankalain da ya faru ranar Jumma'a, inda wasu mutanen fiye da 400 suka samu raunika.

Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka, tana cikin rudanin siyasa tun bayan kifar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011, kuma cikin wtaan jiya an yi garguwa da Firaministan kasar Ali Zeidan na wani lokaci. Firamnistan ya ce gwamnati tana daukan matakan kawar da daukacin tsageru daga birnin na Tripoli da ke zama fadar gwamnatin kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar