1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTunusiya

Al'umma a Tunisiya sun bukaci a saka ranar zabe

Binta Aliyu Zurmi MNA
May 12, 2024

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka fantsama manya da kananan tinuna suna kira da a sako 'yan jarida da 'yan gwagwarmaya gami da 'yan adawa da mahukuntan kasar ke ci gaba da tsare su ba tare da hukunci ba.

https://p.dw.com/p/4flUH
Tunesien | Umgang mit Migranten
Hoto: Hasan Mrad/ZUMAPRESS/picture alliance

Masu boren ko baya ga haka sun kuma bukaci a gaggauta saka ranar da za a gudanar da babban zabe a kasar da ke arewacin nahiyar Afirka.

Boren na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma ke tsaka da fama da matsin tattalin arziki da ma matsalolin siyasa da suka yi wa kasar katutu.

Karin bayani: Shekaru 12 da juyin-juya halin Tunisiya

A baya hukumar zaben kasar ta yi alkawarin gudanar da zabe a kan lokaci, to sai dai har yanzu da wa'adin Shugaba Kais Saied da aka zaba a shekarar 2019 ke gaba da cika, hukumar ta gaza saka ranar yin zabe.

Masu boren sun yi kira da a tsaftace fagen siyasar kasar da ma ba da damar fadin albarkacin baki.