1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya: Zanga-zangar adawa da gwamnati

March 4, 2023

Babbar kungiyar kwadago ta kasar Tunisiya ta gudanar da zanga-zanga a babban birinin kasar Tunis, domin nuna adawa ga gwamnatin shugaba Kais Saied.

https://p.dw.com/p/4OFr4
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Kais Saied
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Kais SaiedHoto: Jihed Abidellaoui/REUTERS

Zanga-zangar ta kasance mafi girma tun bayan da shugaban kasar Kais Saied ya kame 'yan adawan kasar, a wani shirin sauye sauye mafi girma ta fuskar siyasa tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2011.

Dubban jama'a ne suka fito kan titunan Tunis babban birnin kasar dauke da kwalaye suna cewa ba ma son mulkin mutum daya, tare da yin Allah wadai da rundunar 'yan sandan kasar.

Shugaban kungiyar kwadagon, Noureddine Taboubi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da 'yanci da walwalarsu a kasar. Masu boren da dama dai na cewa, sun dauki wannan mataki ne domin nuna adawa ga mulkin shugaba Saied na kama karya. A baya-bayan dai rundunar 'yan sandar kasar ta tsare gomman manyan 'yan adawa da gwamnati ta zarga da kitsa makarkashiyar da ka iya tada zaune tsaye bayan sun shirya gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi.