1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu aikin ceton Italiya sun tabbatar da mutuwar mutane takwas

December 29, 2014

Mutane takwas suka hallaka a jirgin ruwan fasinja da ya kama da wuta

https://p.dw.com/p/1EC7y
Brand auf Fähre in der Adria Norman Atlantic 29.12.2014 Rettung
Hoto: Reuters/Marina Militare

Masu aikin ceto sun gano gawawaki takwas, yayin da suke ci gaba da duba ko akwai sauran mutane daga cikin jirgin ruwan fasinja da ya kama da wuta daga kasar Girka zuwa Italiya.

Mahukuntan kasar Italiya sun bayyana kammala aikin ceton inda aka ceto mutane 427 da suka hada da ma'aikatan jirgin ruwan 56, kamar yadda ministan sufuri na kasar Maurizio Lupi ya tabbatar. Sai dai minista Lupi ya ce ana ci gaba da yuwuwar mutanen da suka bace a cikin jirgin, saboda bayanai sun nuna kimanin mutane 478 da ke lokacin da hadarin ya faru.

Tuni masu gabatar da kara a gaban ruwan Bari na kasar Italiya sun bude bincike kan yadda jirgin ruwan fasinja na Norman Atlantic ya kama da wuta, domin duba yuwuwar sakaci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar