Masar za ta saki dan jaridar Aljazeera | Labarai | DW | 23.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar za ta saki dan jaridar Aljazeera

Wata kotu a kasar Masar ta ba da umarnin sake Mahmoud Hussein bayan shafe sama da shekaru uku a gidan yari bisa zargin yada labaran karya da bata sunan kasar Masar a duniya.

Gidan talabijin na Aljazeera mai cibiya a birnin Doha ta tabbatar da sake ma'akacinta a shafinta na internet, Aljazeera ta zargi hukumomin kasar da kama dan jarida Mahmoud Hussein ba tare da hujjoji ba.

Tsawon kwanaki 881 da Husein ya yi a tsare gwamnatin Masar ba ta gabatar shi ba a gaban shari'a ba, sai dai 'yar Mahmoud Hussein ta ce za a saki mahaifin nata ne bisa wasu sharuda.

A watan Disamban shekarar 2016 ne hukumomin kasar Masar suka kama dan jaridar a filin jirgin Cairo bayan dawowarsa gida daga hedikwatar ofishin Aljazeera da ke birnin Doha a kasar Katar.

Tun bayan juyin juya hali a aksar Masar a shekarar 2013, gwamnati ta kama masu fafutika da dama ciki har da 'yan jaridu bisa zargin taimaka wa kungiyar 'yan uwa musulmi, sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam na sukar yadda gwamnatin ke take hakkin 'yan jaridu.