Masar za ta maida huldar jakadanci da Libya | Labarai | DW | 16.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar za ta maida huldar jakadanci da Libya

Masar ta ce ta fara shirin bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar Libiya a karon farko cikin shekaru shiddan da suka gabata.

Wannan shiri na bude ofishin da aka fara yinsa ya biyo bayan tattaunawa da aka yi tsakanin jami'an kasashen biyu a jiya Litinin da kuma yau Talata kamar yadda kamafanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Masar na daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen ba da goyon baya ga Janar Khalifa Haftar da a baya yake da gabashin kasar, sai dai ga alama ta sassauto daga wannan matsayin bayyan da aka samu amincewar girka gwamnati a Libiya wadda ta samu karbuwa daga bangarorin kasar da ke gaba da juna.